ABNA24 : A wani biki da shugaban kasar, Hassan Ruhani, ya jagoranta ta kafar bidiyo, an nuno sabbin na’u’rorin samfarin IR-6 su 164 wadanda suka ninka tsofafin na’urorin da Iran ke amfani dasu kafin cimma yarjejeniyar nukiliyar 2015, samfarin IR-1, karfi sau goma.
Haka kuma Iran, ta kaddamar da aikin wasu na’u’rorin samfarin IR-5 su talatin, a tashar nukiliyar ta ta Nantaz dake tsakiyar kasar.
Wani abu da ya fi daukan hankali, shi ne yadda gidan talabijin din kasar ya nuno wasu manyan na’urorin tace sinadarin na uranium samfanin IR-9, wanda ya fi karfin samfarin IR-1 sau 50.
An nuna wadanan na’urorin ne a yayin zagayowar ranar kasa ta fasahar nukiliya.
Wadannan nau’urorin da shugaban kasar ya ce yanzu haka suna kan waji ne, zasu iya baiwa Iran damar gaggauta tace sinadarin uranium dinta a mataki mai yawa.
Shugaba Ruhani, ya kuma jadada ecwa shirin nukiliyar kasarsa na zaman lafiya ne.
342/